- Fitaccen ɗan jarida kuma shahararren marubuci cikin harsunan Turanci da Hausa Tijjani Muhammad Musa wanda aka fi sani da laƙanin Poetic Tee a duniyar adabi musamman a fagen rubutattun waƙoƙin Turanci (poetry) sannan kuma ake kiran shi da Muhammad Tajajjini ɗan Tijjani a fagen adabin Hausa ya samu nasarar ciyo wata lambar yabo mafi ƙololuwar daraja wato “Distinction” a wata gasa da aka gudanar a wani dandalin sada zumunta na yanar gizo.
Wannan gasa da dandalin sha’iran rubutattun waƙoƙin Turanci dake da mambobi daga ko’ina a faɗin duniya mai suna Beautiful Minds Community MMXVI sun shirya kuma sun gudanar da shi a makon 6-13 ga watan Satumba, 2025 don a taya su murnar cika shekaru tara (9) da kafuwa.
Dandalin da mambobinsa kan rubuta waƙoƙin Turanci cikin salo dabandaban a wannan karon sun nemi a rubuto waƙoƙin shiga gasar ne ta sigar “Acrostic poem” wato a yi amfani da haruffofin wata kalma a ƙirƙiri waƙa wacca za ta nuna farin cikinsu ta yabi tafiyarsu ta kuma nusar da su inganta tafiyar.
An zaɓawa marubuta gasar kalmar “ANNIVERSARY” bi ma’ana bikin taya murnar cika wasu adadin shekaru ana tafe da wata manufa a ƙungiyance. Akan haka ne aka ba wa kowa damar ya je ya ƙirƙiro abin da fasaharsa ta taya shi bijirarwa.
Bayan alƙalan gasar sun kammala tantance waƙoƙin don tabbatar da sun cika dukkan sharuɗɗa, dokoki da ƙa’idojin da aka gindaya wa ƴan takarar sai suka fid da zakarun gasar inda waƙar da Tijjani wanda ya wakilci Najeriya ta fito a rukunin waƙoƙin da suka fi sauran yin zarra a gumurzun da aka tafka.
Daga cikin dubban rubutattun waƙoƙin da mawaƙa suka shigar gasar guda ashirin (20) ne kacal suka kai da bantensu. An kuma kasa waɗannan zaɓaɓɓun waƙoƙi guda 20 gida uku. Rukunin farko na ƴan Distinction su takwas (8) ne kuma su ne waƙoƙi mafi kyau da karɓuwa da tasiri a hukuncin alƙalan dangane da samun cika da kamala.
Sai rukunin da ke biye da su wato ƴan “Excellent” su ma su takwas (8) ne wanda suka cika ka’idoji da sharuɗɗa sai ɗan rauni da suke da su na inganci da tsaruwa da ba da ma’ana. Rukuni na uku kuwa na ƴan ba yabo ba fallasa ne su huɗu (4). Wato ƴan “Appreciation” waɗanda aka yiwa jinjina da kyakkyawan ambato.
Waƙar da ɗan Tijjani ya shigar ta samu fitowa a ajin Distinction wato ɗaya daga cikin 8 na farko. Wannan dalilin ne ya sa hukumar dandalin ta ba sha’irin shaidar karramawa mafi ƙololuwa a rukunin da shi da kasarsa Najeriya suka fito.
Ga masu son su karanta waƙar da Tijjani M. M. ya shiga gasar ga zubinta amma fa a cikin harshen Ingilishi:
SUNA: Tijjani Muhammad Musa
ƘASA: Nigeria
SALO/TAKE: Acrostic poem: ANNIVERSARY
Another milestone covered
New sun arises to sprint on
Never set on a lovely muse
Infinitely will your words flow
Vastly ventriculating volumes
Enchanting the sad, depressed
Reinvigorating their soul’s soul
Sharing bliss, spreading peace
Across hearts, even blackholes
Rarely will you ever find another
You, a vive, a-thrive, a spirit alive.
©2025 Poetic Tee
Ga kuma sunayen sha’iran da suka samu cin nasara a gasar a kowane rukuni kamar haka:
ƘOLOLUWA (Distinction)
1. Renee Dumond Brown – USA
2. Manohar Luthra – India
3. Tijjani Muhammad Musa – Nigeria
4. Maria Elvira Fernandes Correia – Brazil
5. Richa Anand – India
6. Dr. Prafulla Kumar Panda – India
7. Maricris Cabrera – Philippines
8. Kanakagiri Shakuntala – India
INGANTATTU (Excellence)
1. Krishna Walikar – India
2. Pamie Sandhu – India
3. Robert Bradley – USA
4. Subhaschandra B. Adhav – India
5. Sajid Hussain – Pakistan
6. Manorama Sahoo Subudhi – India
7. Bhagat Subba – Bhutan
8. Sarojini Singh – India
JINJINA (Appreciation)
1. Dr. Raj Karan Dwevedi – India
2. Subhojit Kar – India
3. Shib Raj Pradhan – India
4. Dr. Gregory Elayadom – India
Sa hannun masu tsarawa:
© Angel Rustic Mornin (Shugaba)
Kun ji yadda wannan al’amari ya kasance. Muna taya kowa murna da fatan alkhairi.
Rahoto/Fassara: DWi/SWS.Comms Radio








