A ranar Asabar, 20 ga Satumba, 2025, an yada labarin cewa fitaccen mawakin Hausa, Dauda Adamu Kahutu Rarara, ya samu digirin girmamawa daga jami’ar European-American University a wani taro da aka ce ya gudana a NICON Luxury Hotel, Abuja. Wannan ya jawo cece-kuce a kafafen yada labarai da na sada zumunta, inda mutane da dama suka tofa albarkacin bakinsu kan wannan lamarin.
Sai dai jami’ar ta fito fili ta karyata wannan batu, tana mai cewa ba ta taba shirya ko gudanar da wani taro a Abuja ba, kuma ba ta taba baiwa Rarara ko wani daga cikin sunayen da aka ambata irin wannan digiri ba. A cewar jami’ar, taron da aka yi ya kasance na bogi, tare da yin amfani da sunan makarantar ba tare da wani izini ba. Ta kara da cewa mutanen da suka gabatar da kansu a matsayin wakilan jami’ar ba su da wata alaka da ita, kuma ba su da ikon bayar da kowane irin digiri a madadinta.
Sanarwar jami’ar ta kuma nuna cewa ta dakatar da duk wani aiki da ta ke yi a Najeriya har sai an warware wannan lamari. Haka kuma ta yi gargadin cewa za ta dauki matakan shari’a domin kare martabarta da dakatar da duk wani yunƙurin amfani da sunanta ta hanyar da ba ta dace ba. Duk da haka, jami’ar ta ce idan har wadannan mutanen da ake cewa an karrama suna sha’awar neman digirin girmamawa na gaskiya, za su iya tuntubar ta kai tsaye domin tantance cancantarsu ta hanyar kwamiti na musamman, ba tare da an biya kowane irin kudi ba.
Lamarin ya sake jawo hankalin jama’a kan yawaitar amfani da takardun bogi da digirin karya a Najeriya, al’amari da ke barazana ga martabar ilimi da gaskiyar lambobin yabo daga jami’o’i. Jami’ar European-American University ta jaddada cewa ba ta taba baiwa Rarara digirin girmamawa ba, kuma taron da aka ce an yi domin wannan girmamawa ba shi da alaka da ita kwata-kwata.





