Daga alƙalamin Tijjani Muhammad Musa
A wannan lokacin a dandalin Yanar Gizo ɗaya daga cikin abubuwan da suka fi jan hankali mutane da yawa babu ya zancen kalolin fentin da ake yiwa filoli da wajen makarantun da shahararren ɗan jaridan nan na duniya kuma mai kishin ƙasa da ƙaunar ci gaban al’uma wato Ɗan Bello yake gyarawa ko ginawa.
Tabbas launuka ne da aka saba gani masu kyau da haske da ɗaukar ido da jan hankali da dai sauransu. Kuma tabbas kaloli ne da akan yi amfani da su wajen koyarwa da ilimantar da yara ƙanana saboda muhimmancinsu wajen saurin ɗarsuwa a zukata da ƙwaƙwalen yara in har ana yi musu darussa da su.
Daga cikin bidiyoyin da suka sa Ɗan Bello lokaci ɗaya ya yi shura a idon duniya shi ne wanda ya yi akan lalalallcewar makarantu da ajujuwan koyar da yaranmu a furamare da sakandare ilimi inda ya yi wa al’amari tonon asiri da tonon sililin da abin sai dai a yi tofin ala tsine. Gwamnatoci masu ci da dama abin bai yi musu daɗi ba.
To bayan wannan bankaɗar da Ɗan Bello ya yiwa masu ruwa da tsaki a wannan fanni na ilimi ina kyautata zaton sai ya ƙalubalanci kansa cewa maimakon ya yi terere ya bar zancen haka me zai sa ba zai yi wani abu akai ba. Wato tun da yana da ɗan hali bari ya fara gyara ɓarnar ko a samu ɗan canji da ci gaba akan matsalar har wasu su kama kwaikwayarsa.
Wana tudu wana gangare wannan bawan Allah ya nemi izini kuma an ba shi na ya shigo ya ga abin da zai iya yi akan gyara makarantun nan da yake ta yiwa fallasa a duniya kuma Alhamdulillah rahotannin aiyukansa na gyara makarantun nan da suke fitowa a kafafen sadawar zamani wato su Fesbuk, Insitagiram, Waz’af da dai makamantansu duk sun nuna cewa da gaske ya ke kuma haƙƙansa ya fara cimma ruwa. Alhamdulillah. Ma sha Allah.
Kwatsam! Sai wata ƴar matsala ta wanzu a hotunan bayabayan nan na makarantar da Ɗan Bello da ma’aikatansa suka yi na amfani da launukan fenti dabandaban a wajen ginegine da filolin ginin da suke nuna nasaba da wata tafiya da a wannan bangaren na Arewa da ma al’umar Musulmin duniya ya saɓawa matsaya da aka amincewa.
Wato na gujewa dukkan wani abin da Musulunci da Shari’arsa bai lamuntu da shi ba. Dukkan abin da zai kawo shubha ko waswas ko kokwanto a tunani da addinin musulmi ana son mutum ya kiyaye shi ya guje shi. Ba amfani da kalolin ne aibu ba amma yadda duniya yanzu ta ɗauki waɗannan launuka a tattare a wajen guda shi ne abin dubawa.
Da wasu suka yi jan hankali akan al’armarin sai wasu a dandalin sada zumunta na Fesbuk suke kare abin har ma su ke ganin kamar hassada ko butulci ake nunawa wannan yunƙuri na Ɗan Bello. Wasu kuma suka fito suna cewa sam wannan ba hassada ko ƙyashi ko kushe ko raina masa hoɓɓasansa ba ne. Alhamdulillah kowa na jinjina ƙoƙarinsa kuma ana yaba ķishinsa. Abin sai son barka.
Mutane ba su hana shi yin alkhairinsa ba amma ai Ɗan Bello ba ƙidahumi ko maras ilimi ba ne. In zai yi ya yi daidai mana. Ai ya san ma’ana ko sabuwar manufar waɗannan kaloli a rayuwar zamanin nan. Kar shi da abokan hulɗarsa masu wannan taimakon su shigo wa jama’a da kura da fatar akuya ba su sani ba. Wannan shi ne abin da ake gudu ba zamananci ko wayewa ake ƙi ba.
Yin kaloli irin wannan a zamanin nan ya ɗauki sabon ma’ana don yanzu haka yana da nasaba ne da launukan da ƴan LGBTQ+ suka ƙwata. Idan da ba a sani ba to yanzu kowa ya farga. Sun yi “kidnapping” kalolin Bakan Gizo sun mai da su tambarinsu. Bari dai in yi wa al’umarmu fashin baƙi akan ma’anar haɗakar waɗannan launuka a waje ɗaya a wannan marras.
Bi ma’ana su Ƴan LGTBQ+ suna nufin su mutane ne masu bambanci sha’awe-sha’awe wato wani namiji zalla yake so (gay-luwaɗi) wata mace zalla take harka da (lesbian-maɗigo). Wasu kuwa ko namijin ne ko macen ce babu wanda ba sa harkar saduwa da su (bisexual-ƴan muna biyun).
Wasu kuma ƴan daudu ne wato a tunaninsu su jinsin mata ne a garƙame cikin jikin maza ko akasin haka idan su mata ne ke wannan tauyayyen tunanin (transsexuals/gender) Don haka su kan ɓad da kama su sa suturar maza ko ta mata su yi kwalliya da jambaki da hoda da jagira da dai sauransu su rikiɗa su koma mata.
Kai da yawa ma su kan sa rigar nono su yi cushen nono su sa gashi (wigs) da mazaunai su saka takalmi ɗagogoɗago su kashe muryar suna tafiya suna rangwaɗa wAllahi in ka gansu kai ka ce mace ce ko kuma namiji ne in mace ce ta ke wannan sauya kamar. Sai kuma waɗanda kawai ƴan ganin dama ne. Duk abin da ra’ayinsu ya raya musu to su ne a wannan ranar la ba’asa su haka ne.
Don haka ko da ana amfani da waɗannan kalolin wasarairai don koyarwa ko ilimantarwa a zamanin da to yanzu duk in da ku ka ga an sa launukan nan tare to a lalubi manufa, don abin da ake nufi wajen nan na ƴan LGBTQ+ ne ko kuma ana lale da su.
Da wannan hadakar launukan Bakan Gizo abin nufinsu anan shi ne su ne a madadin kowane launi suka yi haɗaka suke taruwa a waje guda wai don al’uma suna ƙyamarsu ba sa son su ba sa mu’amalar yau da kullum da su yadda ya kamata to su suna son kansu suna ƙaunar junansu yadda suke kuma za su yi gamayya da ƴan uwantakar juna.
Duk wani ko wata waɗanda suke ire-irensu su zo ga gida na LGBTQ+ wato Lesbian (Madigo) Gay (Luwaɗi) Bisexual (Muna biyun) Transexual ko gender (Ŷan daudu) Queer (Boƙararru, Bauɗaɗɗu, Birkitattu)+ (Da dai sauransu) ya samu.
Wato saboda yawansu da bambance-bambancen sha’awe-sha’awensu yau ga shi nan sun kafa ƙungiyar kare haƙƙoƙinsu. Daga nan sai suka ce yadda Bakan Gizo ya haɗa kalolin nan guda bakwai mabambanta to bari su ɗauke shi alama ko tambarin (logo) tafiyarsu. Ta yadda duk inda aka ga haɗakar waɗannan kaloli ko launuka to alamarsu ce.
Wannan shi ne dalilin da ya sa ake ganin bai dace da yiwa ginegine ko ajujuwan makaranta musamman ta yara kai harma da ta manyan irin wannan salon fentin ba. Fentin dai a ɗaiɗaikunsu ko a wawwarensu duka babu wata illa amma a harhaɗe su da wata manufa to ɓoye shi ake nufi da bai kamata ba don kamar ana nunawa bauɗewa da masha’an da ƴan LGBTQ+ suke aikatawa goyon baya ne.
wAllahu a’lam.
(c)2026 Tijjani M. M.
A Kiyayi Haƙƙin Mallaka











